Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bangladesh: Ruwan Sama Ya Haddasa Zaftarewar Laka da Hallaka Mutane 43


Zaftarewar Laka a Bangladesh
Zaftarewar Laka a Bangladesh

Ruwan sama da ya haddasa zaftarewar laka ya kuma yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 43 yayin da mahukuntan kasar Bangladesh suka ce adadin na iya karuwa saboda wasu da yanzu ba'a san inda suke ba.

A ranar Talata hukukumomi sun yi gargadin cewa ta yiwu adadin wadanda suka mutu ya karu yayin da ma’aikatan agaji suka isa unguwanin dake gundumomin dake kan tuddai a kudu maso gabashin kasar.

Lakar ta binne gidaje da yawa bayan da aka fara ruwan jiya Litinin.

Gundumar Rangamati dake kusa da iyakar kasar da Indiya ita ce abin ya fi yi wa lahani.

A watan da ya gabata, wata mahaukaciyar guguwa ta kashe mutane 7, ta kuma lalata dubban gidaje a kudu maso gabashin kasar ta Bangladesh.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG