Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barazana Aka Yi Wa Rayuwata Shi Ya Sa Na Yi Shiru - Stormy Daniels


Stormy Daniels da Donald Trump

An fitar da hirar da gidan talbijin na CBS ya yi da Stormy Daniels, matar da ta yi fice a fannin hada sinima na nuna tsaraici, inda ta bayyana yadda shugaba Donald Trump ya neme ta da kuma abin da ya biyo baya.

‘Yar wasan sinima ta Amurka da ake wa lakabi da Stormy Daniels wacce ke ikirarin ta taba zama budurwar Donald Trump kafin a zabe shi a matsayin shugaban kasa ta fito ta bayyana yadda kawancensu ya kasance.

Daniels ta shaidawa shirin “60 Minutes” na tashar talbijin ta CBS a cewa an yi wa rayuwarta barazana a lokacin da ta yi yunkurin fadan labarinta.

Ta kuma ce ta karbi kudaden “rufa-rufa” masu tsoka daga lauyan Trump domin ta na tsoron abin da zai samu iyalinta.

Stormy Daniels, wacce asalin sunanta shi ne Stephanie Clifford, ta bayyana a jiya Lahadi, a zaman hirar da aka dade ana jira cewa, ta na kan hanyar zuwa wajen motsa jiki ita da ‘yar ta a lokacin da wani da ba ta san ko wane ne ba a zo ya same ta.

Ta shaidawa dan jarida Anderson Cooper cewa “wannan mutum ya zo ya same ta ya ce, ki rabu da Trump, ki manta da labarin.

A cewar ta mutumin ya kuma a kalli 'yarta ya ce bai zai yi kyau wani abu ya sami mahaifiyar wannan kyakkyawar yarinya ba, inda daga baya sai ya bar wajen.

Lamarin dai ya faru ne a wani wajen ajiye motoci a Las Vegas a 2011 ya faru ne jim kadan bayan da ta yi kokarin siyar da labarinta ga wata jaridar tsegumi.

Ta ce lamarin ya tsorata ta mutuka, dalilin da ya sa ta ga kamar karbar kudi har dalar Amurtka 130,000 daga lauyan Trump, Michael Cohen shi ne ya fi.

Tuni dai shi lauyan na Trump, Cohen, ya musanta cewa an yi wa Daniels wata barazana.

Sannan ya ki amsa gayyattar da masu shirya shirin na “60 Minutes” suka yi mishi na ya zo shi ma ya gabatar da na sa bahasin.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG