Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana'izar Matar Tsohon Shugaban Amurka Bush


Jana'izar Barbara Bush
Jana'izar Barbara Bush

Tsofin Shugabannin Amurka da dama na daga cikin daruruwan masu makoki da kuma addu’ar bankwana a yau dinnan Asabar ga marigayiya Barbara, matar tsohon Shugaban Amurka George H. W Bush, wadda ta rasu ranar Talata da shekaru 92.

Ita ce matar Shugaban Amurka na 41, George H.W. Bush, kuma mahaifiyar George W. Bush, wanda shi kuma ne Shugaban Amurka na 43.

Baya ga mijinta da kuma dan farinta, Barack Obama da Bill Clinton na daga cikin tsofin Shugabannin kasar da su ka halarci jana’izar marigayiya Barbara Bush a Majami’ar St. Martin’s Episcopal a birnin Houston da ke jahar Texas na kudancin Amurka.

Melania Trump, matar Shugaba na yanzu da matan tsoffin shugabannin Amurka su Michelle Obama da Hillary Clinton su ma sun hallara.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG