Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan Nada Manyan Jami'an Tsaro Sai Kawar da Hanyoyin Barna Kafin Ministoci-Garba Shehu


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Biyo bayan nada manyan hafsoshin Najeriya da mai bada shawara Muryar Amurka ta zanta da mai magana da yawun gwamnatin Buhari akan wasu muhimman batutuwa

Abokin aiki Bello Galadanci ya fara tambayar Malam Garba Shehu mai magana da yawun gwamnatin Buhari dalilin sauke hafsan hafsoshi da shugaban ya yi.

Malam Garba Shehu yace abun da shugaba Buhari yayi ba sabo ba ne. Duk lokacin da aka samu canjin gwamnati da sabon kwamandan dakaru na kasa gaba daya yana da zabi ko ya cigaba da aiki da hafsoshin da ya gada ko kuma ya canzasu da wadanda ya ga zai iya aiki dasu.

Garba Shehu ya jawo hankalin jama'a da su duba su gani wane irin canji ake son a yi domin a yi sabuwar shimfida da samun sabuwar alkibla wadda zata kai ga biyan bukata ba irin ta da can da bata kai kasar koina ba.

Dangane da irin canjin da ake kyautata zato za'a gani Malam Shehu yace an kafa dakarun hadin gwiwa na kasashen dake makwaftaka da tafkin Chadi kuma sai karshen wannan watan ne zasu fara aiki gadan gadan na yakar 'yan ta'adan Boko Haram. Ma'ana sai sun fara aiki za'a fara ganin canji sosai akan harkokin tsaro cikin kasashen da kungiyar ke yawan kai hari.

Akan batun da aka ce wani dan gwagwarmayar kare hakin bil Adama yayi na cewa wai 'yan Boko Haram ashirye suke su sako 'yan matan Chibok idan gwamnati zata sako mutanenta da take rike dasu, Malam Shehu yace basu da wannan labarin.

Akan gano wadanda suke daukan nauyin Boko Haram, Malam Shehu yace yanzu suka fara aiki amma suna jiran taimako daga manyan kasashen duniya akan rahotannin leken asiri da suke dashi. Yace kasashe masu karfin masana'antu irin su Amurka suna da bayanan asiri da zasu iya ba kasar domin taimakawa.

Batun nada ministoci Malam Shehu yace kamar yadda shugaban kasa Muhammad Buhari ya sanar ginin da ya samu rubabbe ne. Kasar ta yi nisa cikin yin barna da dukiyar jama'a. Saboda haka shugaba Buhari ba zai nada ministoci ba cikin wannan yanayin, wato ya dora tubalin gina kasa akan gurbatacan tushe ba tare da yin gyara ba. Sai ya yi gyara tsaf ya sarkake kasar kafin ya nada ministoci.

XS
SM
MD
LG