Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar (EFCC) Tace Akwai Wasu Gwamnonin da Zasu Shiga Komar Ta


EFCC
EFCC

zamu shigar da kara muna son a gurfanar da jamiaan hukuma a kotu

Hukumar EFCC bata musunta cewa wasu tsoffin gwamnoni da dama na jerin wadanda zata yi awon gaba dasu ba.

Kakakin Hukumar Wilson Unwajerem na nuna ba zai bayyana sunaye ko asirin aikin hukumar ba.

Amma ya nanata sam ba wai suna gayyata ko kama wadanda suke tuhuma da almundanahana don su burge shugaba Buhari bane, ya bar shugaban hukumar na yanzu Ibrahim Lamurde bisa mukamin.

‘’Ban gane abinda kake nufiba, wace gwamnatin kake Magana gwamnatin Buhari sam ba haka bane mu dai muna aiki ne bisa kaidar da doka ta shinfida’’.

Na bincika masaukin hedikwatar hukumar inda har zuwa farkon makon nan tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako da dansa Sanata Abdul Azeez ke ci gaba da zama a tsare duk da samun beli daga alkali E S Chukwu na babban kotun tarayya.Kan yarjejeniyar beli kan Naira miliyan dari ukku da hamsin.

Sanata Abdul Azeez dai na ganin sun shiga samun tsangwama ne ba wai don tuhumar al’mundahanan tuhuma ta naira miliyan 40 ba, amma tun lokacin da mahaifin su ya rubuta wasikar zargin tsohuwar gwamnatin Jonathan da halin ko in kula kan boko haram.

‘’Gasikiya abun shine abin dokar kasa munga abu daban-daban a cikin wannan tafiyar tun tsakanin shekarar data wuce har zuwa yau daga lokacin da dai muka fara maganar cewa, Baba Mai Mangwaro musammam ya fara Magana a kawo canji a kasar nan to daga wannan lokacin har yau bamu samu kwanciyar hankali ba, kuma a kowa ne lokaci da abu ta dan fara sai a tura mutanen EFCC suzo su nemi yadda zasu wulakanta mu damu da zuriaar mu karkaf da kuma duk wadanda suke da tunani irin na Baba Mai Mangwaro’’.

Barister Modibbo Bakari na daga cikin Lauyoyin su Nyakon dake ganin zasu dauki mataki kan hukumar ta EFCC.

‘’Ko wane irin zama da ka kara yi a bayan wannan to ya zama an taka doka, to yanzu kamar wannan a dauka EFCC ne suka aje su to duk wata zama da suka kara zama anan akan karya umurnin kotu suke idan hukuma ta taka doka to tana da yanci a matsayin ka na wanda aka take maka hakkin ka, akan karya doka sai ka gurfanad da wannan hukumar a gaban kotu abinda ake kira COMTEMPT PROCEEDING FOR DISOBEDIENCE TO COURT ORDER Kotun tarayya na Abuja ne suka bada wannan umurnin kuma kotun ne zamu koma, zamu je zamu shigar da kara muna son a gurfanad da jamiaan hukuma wadanda suke da wannan hurumi su bi umurnin kotu sai suka yi karan tsaye’’

Shariun da ake ci gaba dasu anan Abuja sun hada dana tsohon gwamna Jihar Imo Ikedia Ohakin, da tsohon shugaban Maaikata Oransaye akan tuhumar lamushe naira miliyan dubu da miliyan dari tara na fansho.

Ga Nasir Adamu El-Hikaya da Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:20 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG