Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikici Ya Sake Barkewa Tsakanin Fulani Da Tibi


Dan Fulani da dabbobinsa.
Dan Fulani da dabbobinsa.

Bayan dan kwanciyar hankalin da aka samu na wasu 'yan kwanaki, wani mummunan rikici ya sake barkewa tsakanin Fulani da Tibi.

Rundunar 'Yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da mutuwar mutane takwas a wani sabon rikici tsakanin Fulani da Tibi a kauyukan yankin kudancin jihar ta Nassarawa wato Awe Kiyana Obi da Doma. Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandar jihar , Idris Kenedy, ya ce an tura ma'aikatan tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa.

Shugaban kungiyar matasa na Tibi, Jihar Nasarawa, Peter Ahemba ya ce fiye da mutane dubu 100 ne suka kaurace wa muhallansu, sun kuma samu gawarwaki 28.Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah a Jihar Nasarawa, Mohammed Hussaini ya zargi mutanen Tibi daga Benue da kashe 'yan Fulani.

.Haka kuma rundunar ‘yansandan jihar Benue ta tabbatar da mutuwar jami’anta 4 a wani hari da tace ‘yan ta’adda ne suka kai musu a garin Anyibe jihar Benue don haka ne aka tura jami’an yan sanda yankin dan bankado wadanda suka aikata ta’asar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG