Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Binciken Kungiyar Amnesty International Ya Bayyana Gazawar Najeriya Wajen Shawo Kan Fyade


Kungiyar kare hakkin bil’adama ta duniya Amnesty International, ta bayyana cewa gazawar gwamnatin Najeriya wajen shawo kan matsalar fyade da sauran laifuka na cin zarafin mata da kananan yara na kara ta’azara sakamokon rashin hukunta masu aikata laifin.

Cikin wani sabon rahoton bincike da kugiyar Amnesty International ta fitar an gano cewar a shekarar 2020 zuwa 2021 an samu matsalar cin zarafi na fyade a Najeriya sama da 11,220 lamarin da ya ke nuni da yadda matsalar ta yi kamari a kasar.

A hirar shi da Muryar Amurka, Awwal Musa Rafsanjani shugaban kungiyar a Najeriya. ya ce, biniciken ya nuna yadda a ke cigaba da yi wa mata fyade ba'a daukan cikakken mataki na gurfanar da waddanan mutane da suke aikata laifukan lalata da fyade, kuma al'umma ba sa iya fitowa su fadi abun da faru.

Duk da cewa a baya Najeriya ta ayyana dokar ta baci ga matsalar cin zarafin mata da kananan yara, sai ga shi matasar ta fyade na neman kai wankin hula dare a kasar, duba da yadda ake ci gaba da fuskantar matsalar da ake dangantawa da rashin daukar hukuncin da ya kamata.

Dakta Halima Sanda dake kare hakkin mata ta yi kari da cewa matan da ma maza har ma da iyayen ake cin zarafin su, amma saboda kulum ana cikin boye-boye don ba'a so na waje su ji don za'a kyamaci 'ya'yan su ko kuma wasu lokutan ma, sai a dora wa yarinyar laifin fyaden.

A bangare guda kungiyar ta bayyana cewa a lokacin kulle na annobar Covid 19, an samu matsalar fyade da dama, kazalika daga cikin wadanda su ka yi korafi yayin gabatar da wannan sabon rahoto sun bayyana cewa, yanayin yadda jami’an yan’sanda ke yin fatali da kararrakinsu ya sa a wasu lokutan mutane su ka gwamace su yi shiru da bakinsu

Mataimakiyar kwamishinan ‘yan sanda Ada Ochiara wanda ta halarci kaddamar da rahoton a madadin babban sifeton ‘yan sandan kasa ta shaida cewan hukumar ‘yansanda tana daukan matsalar fyade da mahimmanci.

Saurari cikakken rahoton cikin a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00


XS
SM
MD
LG