Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Sun Kashe Sojojin Nijar


Sojojin Cadi da Nijar sun kashe 'yan Boko Haram, Maris 19, 2015

Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai wa sansanin sojojin kasar Nijar hari akan wani tsibirin da ke kan tafkin Chadi, harin da ya hallaka sojoji da dama.

Majiyar rundunar sojojin Nijar din tace daruruwan mahara ne akan kwale-kwale masu inji dauke da makamai suka dirar akan tsibirin Karamga da sanyin safiyar jiya asabar.

Ba dai bayanin adadin wadanda suka jikkata, amma wata majiyar jami’an da ba’a fadi sunansu ba, sun ce ga dukkan alamu akwai yiyuwar harin ya yiwa sojojin babbar illa.

Ma’aikatar tsaro ta sojojin tace dama a yanzu haka ana kan kakkabe ‘yan ta’addar ne daga tsibirin tare da hadin guwiwar sojojin kawancen Nijar, Chadi da Kamaru don yakar ‘yan boko haram daga kan iyakokin kasashen.

Majalisar dinkin duniya dai ta bada kididdigar akalla yara Dubu Dari Takwas ne suka rasa matsuguni, wasu kimanin Miliyan Daya da Rabi kuma suka fantsama uwa duniya sakamakon yada manufofin ‘yan kungiyar ta Boko Haram..

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG