Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Kai Hari Nijar


Sojojin Cadi da Nijar sun kashe 'yan Boko Haram, Maris 19, 2015.
Sojojin Cadi da Nijar sun kashe 'yan Boko Haram, Maris 19, 2015.

A yammacin Lahadinnan ne wasu da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kaiwa sojojin Janhuriyar Nijar hari a kusa da garin Diffa. Wannan hari dai yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama, wadanda ba’a tabbatar da jimlarsu ba zuwa yanzu.

Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tuntubi Lawan Bukar, wanda shine Darektan Majalisar Koli ta Sadarwa a Jihar Diffa.

“Lallai gwamnati ta tabbatar da cewa an samu rikici a dajin Dosso misalin kilomita 30 a garin da ake cewa Karanga. Wato lallai gwamnati ma ta bayyana cewa anyi rikicin amma, a takaice sai dai a yanzu babu wanda zai iya ce maka ga abunda ya wakana”, a cewar Mr. Bukar.

Ya kara da cewa “amma har yanzu gwamnati bata fito ba tace ga adadin barnar da aka samu, ko kuma su ‘yan Bokon, ga wadanda aka kashe. Yanzu kowa yana jita-jitan abunda ya faru, kuma kowa yana jiran sakamakon da gwamnati zata fidda.

Lawan Bukar ya kara da cewa jama’a hankulansu ya tashi, musamman ma gani kamar rigingimun Boko Haram din sun zo karshe.

“Gaskiya a yanzu, a Diffa yanda mutane suke magana, domin kowa tsammani yake kamar an kare, yanzu dai kawai abunda mutane suke bayarwa, karfin gwiwa ne suke baiwa jami’an tsaro, yadda dai kar ayi sake su cigaba da irin wannan abunda suka yi na fari.

A halin yanzu dai Shugaban Nijar, Muhammadou Issoufou ya gudanar da taro da hafsoshin tsaro domin tattauna lamarin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:48 0:00

XS
SM
MD
LG