WASHINGTON, DC —
Yanzu-yanzun nan muka sami labarin tashin wani bom a wata kasuwa a Bauchi, biyo bayan bom din da ya tashi a tashar Motar Dukku garin Gombe kasa da awanni goma sha biyu tsakanin su.
Bom din dai ya tashi a kasuwar central Market dake tsakiyar garin Bauchi, an daice mutane sun cika makil a kasuwar.
Babu wani bayani daga bakin hukumomi ko wata kungiya kan daukar alhakin harin. zamu cigaba da kawo muku cikakken rahoto.