Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom Ya Fashe a Ofishin Sojoji


Fashewar bom. (File Photo)

Karo na Biyu Kennan a Kwanaki Hudu.

Wani fashewa mai karfen gaske da ake zato bon ne,daya faru a wani ofishin sojoji dake kan hanyar zuwa Biu, a garin Gombe ya haifar da tsoro da firgici a tsakanin alumar garin.

Inji cewar mutane da suka ga fashewar, sun bayana cewa bayan fashewar sunji karan harbe-harben bindiga wanda ya tilasa masu neman mafaka.

Kawo yanzu babu cikaken addadin mutanen da suka mutu ko kuma wadanda suka jikirta.

A gefe guda kuma wata majiya daga barikin sojojin,na bayani cewa wata mace ne ta rugumi wani soja da bom a jikinta nan take bom din ya fashe.

Bom din ya hallaka matan da kuma soja da ta ruguma.yayin da wasu sojojin kuma suka samu rauni,a halin yanzu hukumomin soji basu ce komai ba, wannan shine karo na biyu da ake samun fashewa a cikin garin Gombe a kwanki hudu.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG