A lokacin da bom din ya tashi akwai jami’an tsaro uku dake gadin, gidan Gwamna, a cikin motar da aka jefawa bom din.
Abin mamaki shine ba kowa ne zai iya isa inda motar mai silke take ba saida izini domin bangaren da jami’an tsaro suke ne.
Bayan faruwar tashin bom din gwamna jihar ya shiga cikin gidan amma har yanzu babu wani jawabi daga Gwamnatin jihar ta Gombe dangane da wannan.
Idan ba’a manta ba a lokacin karban gaisuwa da kuma jana’izar sarkin Gombe Alhaji Shehu Abubakar, an dauki tsauraren matakai na tsaro saboda manyan bakin da suka je Gombe.