Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bom ya Tashi Bayan Rufe Tafsirin Azumi


Kaduna, ga 23 Yuli 2014.

Akalla mutane 25 suka mutu wasu da dama kuma suka jikita.

Akalla mutane 25 suka mutu wasu da dama kuma suka jikita sanadiyar fashewar Wani bom a kusa da ayarin motocin Sheikh Dahiru Usman Bauchi bayan da aka rufe tafsirin bana, a dandalin Murtala square dake Kaduna.

Bom din ya tashi ne a yau laraba da misalin karfe daya na rana jim kadan bayan da aka tashi daga taron rufe karatun, lokaci da sheikh dahiru bauchi ke kan hanyarsa ta komawa gida.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna Umar Usman Shehu, ya tabbatar da afkuwar lamarin ya kuma kara da cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta daukin kwararan matakan tsaron a wurin taron.

Shima shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta kasa reshen arewa maso yamma Alhaji Musa Ilala ya tabbatar da adadin wadanda suka mutu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:42 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG