Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Ce Ba Shi Da Niyyar Yin Tazarce, Ya Gargadi Masu Ta Da Zaune Tsaye


Shugaba Buhari (Twitter/ @BashirAhmaad)
Shugaba Buhari (Twitter/ @BashirAhmaad)

Shugaban ya ce, “nan ba da jimawa ba, za mu zafafa” matakan da gwamnati ke dauka a fannin tsaro.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa za ta dauki duk matakan da suka dace wajen ganin ta tallafawa hukumar zabe ta INEC don ta samu damar gudanar da ayyukanta.

Buhari ya ce gwamnati za ta ba hukumar duk kayayyakin aikin da take bukata a zabukan da za a yi, saboda kada "wani" ya yi tunanin gwamnatinsa na so ta ci gaba da mulki.

“Ina mai ba ku tabbacin cewa, wannan gwamnati za ta taimaka da duk abin da kuke bukata, saboda kada mu ba da wata kofa, da za a yi zargin cewa, ba ma so mu tafi, ko kuma muna so mu yi tazarce.” Buhari ya ce.

Kalaman shugaban na zuwa ne yayin da shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya kai masa ziyara a fadarsa a ranar Talata.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu (Instagram/inecnigeria)
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu (Instagram/inecnigeria)

Farfesa Mahmood ya kai ziyarar ce don ya sanar da Buhari halin da hukumar ke ciki, inda ya tabo batun hare-haren da ake kai musu.

Sai dai yayin jawabinsa, shugaban na Najeriya ya kara da cewa, “nan ba da jimawa ba, za mu zafafa” matakan da gwamnati ke dauka a fannin tsaro.

Karin bayani akan: IPOB, INEC, Biafra, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

“Wasu daga cikinmu da muka kwashe wata 30 a fagen yakin basasa, muka rika kashe junanmu, akalla mutum miliyan daya. Ta yiwu, wadanda suke ta da zaune tsaye, suna yara kanana a lokacin da hakan ya faru. Saboda haka, za mu bi su ta yadda suke so.” Buhari ya ce.

Sai dai wadannan kalaman na Buhari da ya yi kan yakin basasar kasar, na shan suka daga wasu ‘yan Najeriya, wadanda suka ce bai kamata ya furta su ba, domin a cewarsu, sun keta hakkin bil adama.

“Mun sauya manyan hafsoshi da babban sifeton ‘yan sanda, mun ba su lokacin su kai ziyara sassan kasar, don su yi sauye-sauyen da suka dace, za kuma mu ba su duk irin taimakon da suka nema.”

Babban hafsan sojin kasa, Janar Farouk Yahaya (Twitter/HQNigerianArmy)
Babban hafsan sojin kasa, Janar Farouk Yahaya (Twitter/HQNigerianArmy)

Ya kara da cewa, mutanen da ke yekuwar a yi wa gwamnati bore za su “sha mamaki”, abin da ake ganin alama ce da ke nuna hukumomi za su dauki mummunan mataki akan masu ta da kayar baya a kudu maso gabashin kasar, wadanda ke kai hari ofisoshin ‘yan sanda da na hukumar zabe.

A ‘yan kwanakin nan, ‘yan bindiga sun yi ta kai hare-hare a ofisoshin hukumar ta INEC da na 'yan sanda da ke sassan kudu maso gabashin Najeriyar.

'Yan bindiga suka yi hedikwatar 'yan sanda a Owerri.
'Yan bindiga suka yi hedikwatar 'yan sanda a Owerri.

A makon da ya gabata, hukumar ta ce an kai hari akan ofishinta 41 a jihohi 14, mafi akasarinsu a kudu maso gabashi.

Ana dora alhakin hare-haren ne akan kungiyar IPOB da hukumomin kasar suka haramta, amma kungiyar kan musanta hannun a ciki.

IPOB na fafutukar kafa kasar Biafra ne, a wani mataki na bangarewa daga Najeriya.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG