Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Jinjina Wa Babban Janar Rundunar Sojin Najeriya Da ISWAP Suka Kashe


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi matukar bakin ciki da jin labarin rasuwar Birgediya Janar Dzarma Zirkusu tare da wasu sojoji hudu da suka bayar da sadaukarwa a wani abin da ba a saba gani ba a lokacin da suke yunkurin karafafawa ‘yan uwansu wajen yaki da ‘yan ta’adda.

“Najeriya ta yi rashin jaruman sojoji. Na sara wa jaruntakarsu. Allah Ya Jikan su da rahama. Janar Zirkusu ya bar mu da bakin ciki da bacin rai.” Inji Shugaban.

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka kashe wani Janar din sojan Najeriya da sojoji uku a wani hari da mayakan kungiyar ISWAP da ke yankin yammacin Afirka suka kai a arewa maso gabashin kasar, kamar yadda rundunar sojin kasar ta bayyana.

Kungiyar ISWAP ta balle ne daga kungiyar Boko Haram shekaru biyar da suka gabata kuma tun lokacin ta ke ta yaki da sojojin Najeriya.

Kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya ce sojojin sun yi arangama da ne mayakan ISWAP a karamar hukumar Askira Uba da ke jihar Borno, inda aka gwabza kazamin fada tare da kashe mayakan da dama.

“Abin bakin ciki shine, wani babban hafsan sojoji, Birgediya Janar Dzarma Zirkusu da sojoji uku sun yi sadaukarwa mafi girma yayin da suke yunkurin karfafawa sojojin a farmakin da suka kai wa ‘yan ta’adda,” in ji Nwachukwu a cikin wata sanarwa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce jihar Borno na cikin tsakiyar hare-haren masu tsattsauran ra'ayin Islama, wanda ya addabi kasashen Chadi da Kamaru da ke makwabtaka da Kamaru, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 300,000 da miliyoyin mutane da ke dogaro ga taimakon jin kai.

Majiyoyin soji da mazauna yankin sun ce mayakan na ISWAP sun kai hari Askira da safiyar Asabar da motoci akalla 12 tare da kona gidaje, shaguna da makaranta, lamarin da ya tilasta gudun wasu mazaunan garin.

Askira dai yana da tazarar kilomita 150 kudu da Maiduguri babban birnin jihar Borno kuma yana kan iyakar dajin Sambisa, sansanin mayakan Boko Haram da ISWAP.

Majiyoyin tsaro sun ce mayakan na ISWAP sun kuma kai hari daban-daban a kusa da garin Maiduguri, sai dai kawo yanzu babu cikakken bayani kan asarar rayuka.

Rundunar sojin Najeriya ta ce a watan da ya gabata ta kashe sabon shugaban kungiyar ta ISWAP a wani harin da sojojin suka kai, makonni bayan sanarwar da mutuwar tsohon shugaban kungiyar Abu Musab al-Barnawi.

XS
SM
MD
LG