Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudi Mafi Yawa A Tarihin Najeriya


Buhari a lokacin da yake sa hannu.
Buhari a lokacin da yake sa hannu.

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2018 a fadarsa yau Laraba

Shugaba Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2018 wanda kuma ya kasance mafi yawa a tarihin Najeriya a Naira Tiriliyon 9.12 wanda ya haura na 2017 da kashi 22.6 cikin dari sabanin wanda ya mikawa Majalisar Kasa a watan Nuwambar 2017.

Sai a watan Mayun 2018 ne majalisar kasar ta amince da kasafin kudin 2018 bayan yin wasu gyara. Shugaban ya mika kasafin Naira Tiriliyon 8.6 amma Majalisar ta yi karin Biliyan 500. A bayanin da Shugaban kwamitin kasafin kudi yayi wa manema labarai, ya ce, an yi karin miliyan 500 ne domin aiwatar da ayyukan da ake bukata a kasa.

Sai dai shugaba Buhari bai ji dadin yadda majalisar ta rage kudade har kusan Naira biliyan 347 kan wasu manyan ayyukan da ya ke bukatar aiwatarwa. Kamar tashar wutar lantarki ta Mambilla, da gadan Neja ta biyu, da wasu manyan hanyoyi, da layukan dogo , da ayyukan inganta kiwon lafiya da sauransu.

Sannan ya nuna rashin jin dadinsa da yadda majalisar da karawa kanta kudi har Naira biliyan 14.5 ba tare da tuntubar bangaren zartawa ba inda kudinta ya tashi daga Naira Biliyan 125 zuwa Naira biliyan 139.5

Duk da sauye-sauyen da aka yi, shugaban ya ce ya rattaba hannu domin bai son kara kawo tsaiko ga tattalin arzikin kasa sakamakon rashin amincewa da kasafin kudi da wuri. Amma ya na da niyyar yin gyara kan sauye-sauyen da da aka yi ko yin wani karin kasafi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG