Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Tafi Amurka Taron Majalisar Dinkin Duniya


Shugaba Buhari (Facebook/Femi Adesina)
Shugaba Buhari (Facebook/Femi Adesina)

Fadar shugaban kasar, ta ce a ranar Lahadi Buhari ya kama hanyar zuwa kasar ta Amurka don halartar taron na Majalisar Dinkin Duniya wanda za a yi a juko na 76.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya tafi Amurka don halartar taron Majalisr Dinkin Duniya da za a gudanar a birnin New York, in ji fadar shugaban kasa.

Tun a ranar Asabar kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya ce Buhari zai kama hanyar zuwa Amurkar don halartar taron wanda za a yi a karo na 76.

Zai kuma koma Najeriya a ranar 26 ga watan Satumba.

“Shugaba Buhari zai yi jawabi a taron, a muhawarar da za a yi a ranar Juma’a 24 ga watan Satumba, inda zai yi magana kan maudu’in taron da sauran al’amuran da suka shafi duniya.” Sanarwar ta ce.

A Wannan shekarar, taron zai mayar da hankali ne kan yadda kasashen duniya za su farfado daga bala'in annobar COVID-19, sauyin yanayi da kuma kare hakkin bil adama.

Tawagar shugaban na Najeriyar a cewar Adesina, za ta halarci wasu muhimman taruka kamar na zagayowar cika shekara 20 da kulla yarejejeniyar Durban, wanda ya kunshi batutuwan da suka shafi biyan diyya da tabbatar da adalci da daidaito ga ‘yan asalin nahiyar Afirka.

Baya ga haka, tawagar shugaban kasar za ta yi wasu taruka na kasa da kasa tare da wasu shugabannin duniya da na kungiyoyin kasa da kasa.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Georffrey Onyeama, Babban Atoni Janar na Najeriya kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami da Ministar muhalli Sharon Ikeazor na daga cikin wadanda suka rufa wa Buhari baya.

Sauran sun hada da mai ba da shawara kan tsaron kasa, Manjo-Janar Babagana Monguno mai ritaya, Darektan hukumar tattara bayanan sirri Ambasada Ahmed Rufai Abubakar, da shugabar hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje Abike Dabiri-Erewa da kuma babbar mai ba da shawara kan dawwamammun muradin karni na SDG, Mrs. Adejoke Orelope-Adefulire.

Tun a ranar 14 ga watan Satumba a bude zauren babban taron.

XS
SM
MD
LG