Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Yi wa Trump Da Melania Fatan Samun Sauki


Shugaba Trump, dama da takwaran aikinsa na Najeriya Buhari, hagu wata ziyara da Buharin ya kai fadar White a Washington, ranar 30, Afrilu 2018.
Shugaba Trump, dama da takwaran aikinsa na Najeriya Buhari, hagu wata ziyara da Buharin ya kai fadar White a Washington, ranar 30, Afrilu 2018.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya al’umar Amurka yin addu’o’in nemar wa shugaban kasar Donald Trump da uwargidansa Melania lafiya bayan da rahotanni suka nuna cewa sun kamu da cutar COVID-19.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Juma’a, Buhari wanda ya nuna alhininsa ya ce, “samun bullar cutar a Fadar White House na nuni da irin kalubalen da duniya ke fuskanta kan wannan cuta, da kuma wahalhalun da ke tattare da kokarin da ake yi na dakile yaduwarta.”

Yayin da yake fatan samun lafiya ga iyalan shugaban kasar dangane da wannan rashin lafiya, shugaban na Najeriya ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika kiyaye ka’idojin da ke hana yaduwar cutar.

“Shugaban Najeriya na kira ga ‘yan Najeriya da su kiyaye matakan kariya da aka saka da shawarwarin likitoci da kwararru a fannin annoba.” Sanarwar ta ce.

Da sanyin safiyar ranar Juma’a Shugaban na Amurka ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, shi da mai dakinsa Melania sun harbu da cutar ta coronavirus.

Minti 11 bayan fitar da sanarwar tasa, Fadar White House ta fitar da wata takarda daga likitan shugaban Dr. Sean Conley, wacce ta tabbatar da cewa Trump mai shekara 74 da mai dakinsa sun harbu da cutar.

Tuni Trump da Melania suka killace kansu domin zaman kwanakin da ake bukata mutum ya kadaita kansa bayan kamuwa da cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG