Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burtaniya Za Ta Yi Zaben Raba Gardama Ranar 23 Ga Watan Yuni


Firai Ministan Burtaniya David Cameron

A yau Asabar Firai ministan Burtaniya David Cameron ya bayyana cewa a ranar 23 na watan Yuni mai zuwa, za a yi zaben raba gardama kan ci gaba da kasancewar kasar a kungiyar tarayyar turai ta EU ko kuma akasin hakan.

Yayin da yake ganawa da manema labaria, Cameron ya ce majalisar zartarwa kasar ta amince da ci gaba kasancewar kasar a cikin kungiyar mai mambobi 28.

A cewar Cameron kasar za ta fi samun kariya da karin karfi, idan ta ci gaba da kasancewa a kungiyar ta EU, ya kuma kara da cewa wannan zabe ne da ya rage ga ‘yan kasar ta Burtaniya.

Shi dai Cameron ya ce zai ci gaba da yin kamfen din kasar ta ci gaba da kasancewa a kungiyar.

Matsayar da aka cimma tsakanin Burtaniya da kungiyar ta EU na zuwa ne bayan wani zama da aka yi na gaggawa a Brussels inda aka lamuncin kasar ta Burtaniya kan wasu bukatu da ta gabatar.

Yanzu haka bayanai na nuna alamun cewa an yi raba daidai ne tsakani wadanda suke so a fice da wandanda su ke so a ci gaba da kasancewa a cikin tarayyar ta turai.

XS
SM
MD
LG