Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burundi Na cikin Halin Tsaka Mai Wuya


Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza, wanda ba'a san takamaimai inda yake ba

Sojojin Burundi sun rabu biyu kuma suna fafatawa da juna akan samun iko kan kasar

A Burundi, ofishin shugaban kasar ya bada labarin cewa shugaba Pierre Nkurunziza, ya koma cikin kasar, ofishin yana mai cewa yunkurin juyin mulkin da aka shirya yayinda yake kasar Tanzania bai sami nasara ba.

Ofishin Mr. Nkurunziza ya fada jiya Alhamis cewa shugaban ya jinjinawa sojoji da 'yansanda da kuma jama'ar kasar. Sanarwar tace jami'an tsaro suna farautar wadanda suka shirya juyin mulkin domin a hukunta su.

Babu halin tantance ko shugaban ya koma Burundi, ko kuma ainihin abunda yake faruwa a cikin kasar.

Har zuwa safiyar jiya Alhamis, wasu bangarorin biyu na sojoji suna fafatawa da juna domin iko kan babban birnin kasar Bujumbura. Ana gwabza fadan ne kusa da tashoshin talabijin da gidan rediyo na kasar, inda sojoji da suke goyon bayan juyin mulkin suke kokarin kwace tashoshin daga hanun sojojin d a suke biyayya ga shugaban kasar.

Wani kakakin 'yan tawaye daga cikin sojojin ya gayawa sashen Afirka ta Tsakiya na Muryar Amurka cewa masu biyayya ga shugaba Nkurunziza sune suke rike da tashoshin yada labaran. Yace masu goyon bayan juyin mulkin sun janye daga yankin.

Tashar gidan rediyon kasar da ya dakatar da gabatar da shirye shiryensa na tsawon sa'a daya da rabi, ya cigaba da gabatar da shirye inda masu sauraro suka bayyana cewa tashar tana gabatar da wakokin hadin kan kasa.

A Washington kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Jeff Rathka yace Amurka ta san Mr. Nkurunziza a matsayin halattacen shugaban Burundi, daga nan ta kirayi duka sassan biyu su kaucewa tada tarzoma kuma su kiyaye hakkin Bil'Adama.

Tsohon shugaban hukumar leken asiri na kasar Janar Godefroid Niyombare ne yayi amfani da tashoshin rediyo masu zaman kansu wajen ayyana hambara shugaban kasar ranar Laraba. Idan za'a iya tunawa dai cikin watan Feburairun bana ne aka koreshi daga kan mukaminsa.

XS
SM
MD
LG