Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wa Ke Rike Da Ikon Burundi?


Daya daga cikin masu zanga zangar nuna adawa da burin shugaba Nkurunziza ya tsaya takara a karo na uku

Rahotann daga Bujumbura, babban birnin Burundi na cewa an kwana ana jin harbe-harbe kwana daya bayan da wani babban jami’in sojan kasar ya yi yunkurin hambarar da gwamnatin kasar yayin da shugaban ke wata kasar.

Har yanzu dai babu tabbacin wake iko da kasar yayin da zanga-zangar siyasa da ake yi kullum a Bujunbura ke haddasa fada tsakanin bangarorin jam’iyyun adawa.

Wadanda suka shaida laamrin sun ce an gwabza mummunan fada yau Alhamis a kewayen ginin gidan redyo da na talibijin din kasar, wanda har yanzu ya ke hannun masu goyon bayan shugaban.

Kuma sashen tsakiyar Afrika na nan Muryar Amurka ya ba da rahoton cewa an rufe gidan rediyon Burundi wanda ke mallakar gwamnati.

Tunda farko, gidan rediyon ya gabatar da sakon shugaba Pierre Nkurunziza, wanda ya ce har yanzu shi ne yake kan mulki kasar kuma sojojin kasar suna goyon bayansa.

Babu tabbacin inda shugabaNkurunziza yake yayin da kamfanin dillancin labaran Faransa ya fadi cewa shugaban na wani wuri da ba’a fadi ba a birnin Dar es Salam na kasar Tanzaniya, inda ya halarci wani taron kasashen yankin game da al’amarin siyasar kasar jiya Laraba.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG