Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Canada Ta Jaddada Kudirin Aiki Da Najeriya Don Tunkarar Matsalar Safarar Mutane

Canada Ta Jaddada Kudirin Aiki Da Najeriya Don Tunkarar Matsalar Safarar Mutane Da Kaura Ba Bisa Ka'ida Ba
Canada Ta Jaddada Kudirin Aiki Da Najeriya Don Tunkarar Matsalar Safarar Mutane Da Kaura Ba Bisa Ka'ida Ba

Jakadan kasar Canada a Najeriya Mr. Jammie Christoff ya bayyana hakan ne yayin da ya ke magana a wani taron hadin gwiwa tsakanin Najeriya da kasar ta Canada, don karfafa matakan hadin kai na tunkarar kalubalen safarar mutane da yin kaura ba bisa ka’ida ba.

ABUJA, NIGERIA - Yana jaddada cewa kasarsa za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da gwamnatin Najeriya da sauran hukumomin dake yaki da fataucin mutane da ma cibiyoyin kasa da kasa, don karya lagon kungiyoyin masu fataucin mutane a matakin kasa da kasa.

Ire-Iren mutanen dake safarar ‘dan' adam na amfani da raunin mutanen ne inji jakadan na Canada, wanda ya kara da cewa wannan babbar matsala ce a duniya baki daya, amma girmanta a Najeriya ya shafi mutane da dama.

Jakadan na Canada ya ce a Najeriya suna aiki da hukumar NAPTIP da cibiyoyin kasa da kasa, ba ma kawai wajen gano tare da wargaza masu safarar mutanen ba, amma wajen yiwa tufkar hanci ta hanyar yi mata kandagarki.

Canada Ta Jaddada Kudirin Aiki Da Najeriya Don Tunkarar Matsalar Safarar Mutane Da Kaura Ba Bisa Ka'ida Ba
Canada Ta Jaddada Kudirin Aiki Da Najeriya Don Tunkarar Matsalar Safarar Mutane Da Kaura Ba Bisa Ka'ida Ba

Mr. Jammie Christoff ya ce suna aiki da kuma samar da kudaden tallafi wajen horas da jami'an hukumar NAPTIP a fannin yin kaura, wayar da kai don tunkarar yaki da bautar da mutane a zamanance da safarar mutane, inda ya jaddada cewa kawancen dake tsakanin Najeriya da kasarsa zai taimaka kwarai wajen cimma manufar.

Tunda farko, Darakta Janar na hukumar yaki da fataucin mutane ta Najeriya wato NAPTIP, Farfesa Fatima Waziri Azi, ta yabawa kasar Canada bisa dimbin gudunmuwar da take baiwa Najeriya a fannin shawo kan matsalar safarar mutane, wanda ta ce daya ne daga cikin manyan laifukan dake take hakkin bil'adama dake zama na biyu a duniya cikin manyan laifukan da suka fi samar da kudi.

Canada Ta Jaddada Kudirin Aiki Da Najeriya Don Tunkarar Matsalar Safarar Mutane Da Kaura Ba Bisa Ka'ida Ba
Canada Ta Jaddada Kudirin Aiki Da Najeriya Don Tunkarar Matsalar Safarar Mutane Da Kaura Ba Bisa Ka'ida Ba

Ta ce a bara kadai an sami rahoton safarar mutane sau 1,440 an kubutar da mutane 2,743 kana a bara kotuna sun daure mutane 80 bisa laifin safarar mutane watanni biyun wannan shekara kuma, mutane goma sha bakwai aka yankewa hukuncin.

‘Yan Najeriya da dama dai na ganin kasar Canada tamkar aljannar duniya, inda galibin matasa keta jefa rayuwarsu cikin garari wajen fafutukar yin kaura ta haramtacciyyar hanya zuwa can, yayin da a daya bangaren kuma wasu haramtattun kungiyoyi ke safarar mutane ba bisa ka'ida ba, zuwa Canadan da nufin samun ingantacciyyar rayuwa, da hakan ke zama da hatsari.

Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:

Canada Ta Jaddada Kudirin Aiki Da Najeriya Don Tunkarar Matsalar Safarar Mutane Da Kaura Ba Bisa Ka'ida Ba .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

XS
SM
MD
LG