Accessibility links

Canza Sheka na Cigaba a Majalisar Wakilai Amma Banda ta Dattawa


Ginin Majalisun Dokokin Najeriya

Kawo yanzu kakakin majalisar dattawa bai bayyana sunayen sanatoci 11 da suke ce sun koma APC ba yayin da a majalisar wakilai wasu biyar sun koma PDP

Jam'iyyar PDP ta sake zama jam'iyyar dake da rinjaye a majalisar wakilai yayin da wasu wakilai biyar daga APC suka koma jam'iyyar.

Wannan canza sheka da 'yan majalisar wakilan suka yi ya sa yanzu PDP tanada wakilai 178 yayin da APC ke da 158. To sai dai wani dan majalisar daga jihar Borno kuma dan APC Abdurahaman Terab ya karyata maganar rinjayen PDP din. Yace "Ba gaskiya ba ne a zo a zauna a kirga" Da wakiliyar Muryar Amurka ta tambayeshi nawa suke sai yace "Ai dama na ce maki muna 174 yanzu ya sauka zuwa 159. Idan kuma kin hada da wancan shi ne 158. Amma a zo a zauna a kidaya shi ne gaskiyan abun"

Shi kuwa Umar Bature daya daga cikin wadanda suka bar APC zuwa PDP ya fadawa wakiliyar Muryar dalilinsa na barin APC. Yace "A gaskiya dalilaina na barin APC naga alamun babu adalci. Ba za'a yi mani adalci yadda ake gudanar da jam'iyyar. Nayi kuka nayi kuka na cewa a gyara ba'a gyara ba shi ya sa nace bari in koma inda na sani" Da aka tambayeshi ko a jam'iyyar PDP akawai adalci? Sai yace "To ya dai fi inda ake internal democracy ...inda mutum guda zai iya cewa ga abun da za'a yi ga abun da ba za'a yi ba" Dangane da cewa wasu na ganin jam'iyyar PDP daya take da APC sai yace "E to amma PDP suna dan bamu dama. Nayi wannan a 2011 na ka da dantakara to ban yi tsammanin zan samu wannan adalcin ba yanzu in na je APC"

To a majalisar dattawa kuma sanatoci 11 daga PDP da suka ce sun koma APC basu ji dadi ba domin kakakin majalisar Sanato David Mark yace shi ba zai bayyana aniyarsu na canza sheka ba kamar yadda suka bashi a rubuce sai kotu ta yanke hukunci a kan batun.

Sai dai Sanato Haruna Goje daga Gombe kuma daya daga cikin wadanda suka nemi su canza sheka ya nuna shakku a kan dalilan da shugabansu David Mark ya bada. Da yake mayarda martani Sanato Haruna Goje yace "Ina ganin yana anfani da maganar kotu ne ya ki yin abun da ya kamata yayi. Domin maganar kotu lauyoyinmu tare da mu da na wakilai suka tafi suka wakilcemu. Da mu da na wakilai lauyoyinmu daya. Magana daya ce, tana gaban alkali. Amma wannan bai hana majalisar wakilai tana karanta wasikun wadanda suna barin PDP zuwa APC ko APC zuwa PDP ba"

To sai dai wata majiya tace su sanatocin suka bata rawarsu da tsalle yayin da suka garzaya kotu suna neman ta hana PDP kwace kujerunsu.

XS
SM
MD
LG