Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Canza Sheka Ya Zama Sara A Siyasar Najeriya


APC, PDP
APC, PDP

A Najeriya yadda ‘yan siyasa ke canjin sheka tsakanin jam'iyun kasar na son zama tamkar wani sabon salon siyasar kasar, duk da illolin da ke tartare da yin hakan ga tsarin dimokradiya.

A duk lokacin da aka kada gangar siyasa, kama daga zabubukan mukaman jam'iyu, ko na zaben fitar da gwani ko zaben kujerin gwamnati ‘yan siyasa zasu yi ta rabon idanu dubin inda take da mai gare su in babu biyan bukata kuwa sai canjin sheka, kamar yadda ya sha faruwa kuma yake faruwa a Najeriya a matakai daban daban.

Masana kimiyar siyasa na ganin duk da yake canjin sheka dama ce ta dan siyasa amma dai yadda yake faruwa a kasashe masu tasowa kamar Najeriya tamkar ci gaban mai ginar rijiya ne ga tsarin dimokradiya.

Farfesa Abubakar Abdullahi masanin kimiyar siyasa ne a jami'ar Usmanu Danfodiyo. Ya ce a kasashen da suka cigaba, akwai manufofin na gwamnati na jam’iyya wandanda suke da tasiri wanda ke ba 'yan siyasa damar canza sheka.

Duk lokacin da wani dan siyasa ya canja sheka, zai bayar da dalili na yin hakan, sai dai ba lallai ne dalilan da suke bayarwa su gamsar da jama'a ba.

Duk da yake canjin sheka ba zai rasa tasiri ko amfani ba ga masu yin sa, sai dai illolin da yake yi ga tsarin dimokradiya ya fi muni bisa ga amfaninsa a cewar farfesan kimiyar siyasa Abubakar Abdullahi.

Bisa ga yadda tsarin siyasa ke gudana a Najeriya, ba mai cewa ga lokacin da ‘yan siyasa zasu kasance masu akida musamman duba da cewa yanzu kusan shekaru 23 dimokradiya na gudana babu yankewa.

Amma masana sun ce muddin ba tsari aka samar ba mai tabbabtar da ‘yan siyasa na bin akidar jam'iya sau da kafa to za'a dawwama bisa tsarin da ake kai yanzu wanda kuma ke mayar da hannun agogo baya ga dimokradiyar kasar.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00
XS
SM
MD
LG