Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CDC Ta Ce Ko Jonathan Ya Sauka, Ko A Tsige Shi, Ko Kuma


Shugaba Goodluck Jonathan yan ajawabi gaban wakilan jam'iyyarsa ta PDP lokacin wani taron fitar da dan takara a Abuja a 2011

Ibrahim Modibbo, shugaban kungiyar, yace sun ba Goodluck Jonathan mako guda kan yayi murabus a saboda karan tsayen da yake haddasawa a Jihar Rivers

Wata kungiyar kare muradun yankin arewacin Najeriya da ake kira CDC, ta ce lallai shugaba Goodluck Jonathan yayi murabus cikin mako guda, ko majalisun dokokin tarayya biyu su fara daukar matakan tsige shi, ko kuma dai zasu dukufa yajin cin abinci na har sai illa ma sha Allahu.

Shugaban kungiyar, Ibrahim Modibbo, yace sun damu ainun da irin abubuwan da suke faruwa a Jihar Rivers, domin a ganinsu, Goodluck Jonathan da 'yan amshin shatarsa ne suke haddasa wannan rikici, suke gallazawa gwamna Rotimi Amaechi a saboda ganin alamun cewa ba ya goyon bayan Mr. Jonathan ya sake tsayawa takarar kujerar shugabancin Najeriya.

Yace duk Najeriya babu wani gwamnan da ake kuntata masa, kamar gwamna Amaechi, inda har aka zuga wasu 'yan banga suka yi ta jifar wasu gwamnonin jam'iyyar PDP daga arewacin Najeriya wadanda suka je su Fatakwal, babban birnin Jihar Rivers, domin jinjinawa da nuna masa goyon baya.

Yayi watsi da batun cewa kungiyarsu tana neman sanya kafar wando guda da jam'iyyar PDP wadda take ikirarin cewa babu hannun shugaban a wannan lamari na Jihar Rivers, yana mai cewa akwai lokacin da matar shugaban, Patience Jonathan, ta kwace abin magana daga hannun gwamna Rotimi Amaechi, a bainar jama'a, duk da cewa shi zababbe ne, ita kuwa babu mutum guda da ya taba jefa mata kuri'ar zamowa wata jami'ar gwamnati.

Ibrahim Modibbo, yayi cikakken bayani kamar haka.

CDC Ta Nemi Goodluck Jonathan Ya Sauka, Ko A Tsige Shi, Ko Kuma. - 2:44
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG