Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chadi Ta Taimaka Wa Dakarun Yankin Sahel Da Sojoji


Shugaba Idriss Deby
Shugaba Idriss Deby

Shugaban rikon kungiyar kasashen G5 Sahel, Idrss Deby na kasar Chadi ya gudanar da ziyarar wuni a jiya Laraba a birnin Yamai, inda ya yi bankwana ga dakarun kasar ta Chadi a kan hanyarsu ta zuwa yankin da kasashen Nijer, Mali da Burkina Faso ke makwaftaka da shi.

Chadin ta bada wannan agaji ne da nufin karfafa gwiwar rundunar hadin gwiwar G5 Sahel a yakin da ta ke kafsawa da ‘yan ta’addan arewacin Mali.

Lokacin da shugaban kasar Nijer Issouhou Mahamadou da takwaran aikinsa Idriss Deby na Chadi suka isa inda dakarun kasar Chadi suka yada zango a kan hanyarsu ta zuwa fagen daga. Wadannan askarawa, su kimanin 1200, na matsayin wani rukuni na bataliyar da kasar ta Chadi ta yi alkawalin aikewa zuwa yankin da Mali da Nijer da Burkina Faso ke fama da mayaka masu ikirarin jahadi.

Da yake jawabin bankwana a madadin wadannan shugabanni, Ministan Tsaron kasar Nijer, Pr Issouhou Katambe, ya ce “Ya ku hafsoshin kasar Chadi dakaru manya da kanana kyakkyawar niyyar da shugaban rikon G5 Sahel ya nuna ta hanyar sabon salon da ya bullo da shi a wannan yaki ya sa zaku tafi fagen daga inda za ku aikin hadin gwiwa da takwarorinku ‘yan Mali da ‘yan Burkina Faso da ‘yan Nijer cikin yanayin fahimta wanda kuma a matakin farko abin zai gudana akan iyakar wadannan kasashe 3, inda zaku yi rawar daji mai lakabin Operation Sama. Ba ma shakka a kan maganar kwarewa da jarumtarku a kan wannan aiki. Muna da kwarin gwiwar za a sami nasarori.”

A karshen taron shugabannin kasashen G5 Sahel da ya gudana a watan Fabrairun da ya gabata ne kasar ta Chadi ta dauki alkwalin aikewa da wannan bataliya da zummar karfafa wa sojojin Nijer, Mali da Burkina Faso gwiwa a yakin da suke yi da kungiyoyin ta’addanci a iyakar da wadanan kasashe ke makwabtaka.

Idriss Deby ya tabbatar da cewa za a sami kyakkyawan sakamako nan da watan Yuni mai zuwa. Haka kuma ya yi alkwarin zuwa fagen daga domin dafa wa askarawansa a wannan yaki.

Shugaban kasar Nijer, Issouhou Mahamadou, ya karrama Idriss Deby da lambar yabo mafi girma a kasar, saboda abin da ya kira dagewarsa a kan batun tabbatar da tsaro, wanzar da zaman lafiya, samar da ci gaban al’umma da kokarin karfafa hulda a tsakanin kasashe.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ma ya sami irin wannan lambar yabo sakamakon lura da abinda hukumomin Nijer suka kira jajircewarsa akan batun samar da tsaron kasa zaman lafiya da aiyyukan ci gaban al’umma.

Kasar Chadi mai dakaru a rundunar hadin gwiwar kasashen yankin tafkin Chadi ta taka rawa wajen karya lagon kungiyar Boko Haram wanda don haka ake kyautata zaton matakin aikewa da sojojinta zuwa iyakar Mali, Niger da Burkina Faso zai rage kaifin matsalar tsaron da ta yi kamari a yankin Sahel.

Souley Moumouni Barma ya aiko mana da wannan rahoto:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00
XS
SM
MD
LG