Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Na Niyyar Taimakawa Ghana Don Ta Samu Lamuni Daga IMF


Ken-Ofori-Atta da tawaga IMF
Ken-Ofori-Atta da tawaga IMF

Gwamnatin China ta ba da wata kwakkwarar alamar cewa tana son taimakawa Ghana wajen tabbatar da ta samu kudaden da take nema daga asusun ba da lamuni na duniya IMF.

A cewar gwamnatin kasar China, tana da alhakin tabbatar da cewa tattalin arzikin Ghana bai durkushe ba.

Ministan kudi na China Mr.Liu Kun ne ya bayyana haka.

Jaridar yanar gizo ta Myjoyonline, ta ruwaito cewa, Mista Kun ya bayyana cewa, hakan na da nasaba da kwarin gwiwar da suke da shi kan makomar tattalin arzikin Ghana na dogon lokaci.

“Mun san cewa wadannan kalubalolin da Ghana ke fuskanta na gajeren lokaci ne wanda a matsayin mu na ba da rance na gari muka himmantu a shawo kan lamarin.

"Hukumomin kasar China suna da kwarin gwiwa kan tafiyar da tattalin arzikin Ghana da kuma dorewar tattalin arzikin."

Mista Kun ya kuma kara da cewa, "Kasar China ta yi imanin inganta tsarin biyan bashi da kuma ci gaba mai dorewa."

Mista Liu Kun ya yi wadannan kalaman ne yayin da ministan kudi na Ghana, Ken Ofori-Atta ya jagoranci wata tawaga zuwa China domin tattaunawa a kan bashin da China ke bin Ghana na sama da dala biliyan 1.7

Tawagar Ghanan ta hada da manyan jami’ai daga ma’aikatar da jami’an ma’aikaytar harkokin waje da jami’ai daga babban bankin Ghana.

Mista Ofori-Atta ya yi tattaunawar fahimtar juna da kasar China kan sake fasalin bashi tare da neman tabbataci da samun kudi daga shirin Ghana da IMF.

Gwamnati na fatan samun amincewar majalisar dokoki game da kudirin kudaden shiga guda uku wadanda muhimman bukatu ne ga kulla yarjejeniya da IMF.

XS
SM
MD
LG