Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Yanke Wa Wata ‘Yar Jarida Hukuncin Daurin Shekara 4 Kan Rahotannin COVID-19


资料照:上海维权人士、公民记者张展
资料照:上海维权人士、公民记者张展

An yankewa wata ‘yar jarida ‘yar kasar China hukuncin zuwa gidan yari tsawon shekara 4 saboda yadda ta bada rahotanni kai-tsaye daga Wuhan a lokacin da aka samu bullar annobar COVID-19.

Lauyan da ke kare 'yar jaridar ne ya fadi haka a yau Litinin, kusan shekara daya bayan da aka samu bullar bayanan wata cuta mai shafar numfashi da ba a sani ba a tsakiyar birnin na China.

Zhan Zhan, wadda lauya ce a a baya, an yanke mata hukuncin ne a wani dan takaitaccen zama da aka yi a kotun Shanghai saboda zargin ta da tsokano fada da haddasa tashin hankali a rahotannin da ta bada a farkon lokacin da ake cikin rudanin bullar cutar ta COVID-19.

An yada rahotannin da ta bada kai-tsaye da kuma rubuce-rubucen da ta yi a kafafen sada zumunta sosai a watan Fabarairu, abinda ya ja hankalin hukumomi, wadanda suka hukunta wasu masu kwarmata bayanan coronavirus su 8 ya zuwa yanzu.

China ta yaba da yadda ta sami nasarar shawo kan annobar a kasar, ga tattalin arzikinta na farfadowa yayin da galibin kasashen duniya ke fama da matakan kulle masu zafi.

-AFP

XS
SM
MD
LG