Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cibiyar Yaki Da Cutar Kanjamau Ta Kasa A Najeriya Tana Neman Karin Kudi


Ana lura da wata mata mai fama da cutar HIV

Directan cibiyar yaki da cutar kanjamau ta Najeriya –NACA- Prof. John Idoko, yayi kira da a kara bada tallafin kudi domin rage yaduwar cutar HIV a kasar

Directan cibiyar yaki da cutar kanjamau ta Najeriya –NACA- Prof. John Idoko, yayi kira da a kara bada tallafin kudi domin rage yaduwar cutar HIV a kasar.

Professa Idoko yayi wannan kira ne a wajen wani taron kwana daya da aka yi da nufin neman sababbin matakan yaki da kwayar cutar HIV a matsayin mataki na gaba da ya biyo bayan taron da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya halarta kan yaki da cutar kanjamau da ake kira PERP a watan Mayu shekara ta dubu biyu da goma sha biyu.

PERP wani shiri ne da aka kaddamar da nufin yaki da matsalar cutar kanjamau a nahiyar Afrika.

A cikin jawabinshi wajen taron, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana cewa, koda yake Nigeriya tana kokari sosai wajen yaki da cutar kanjamau, duk da haka akwai sauran aikin da ya kamata ayi zuwa 2015. Yace ana bukatar sabon salo a fannin matakan kariya da kuma magungunan jinya, abinda ba zai yiwu ba sai da kudi.

A cikin wannan shekata ta 2013 aka cika shekaru 32 da bullar kwayar na cutar HIV a duniya, kuma a halin yanzu cutar tafi yawa a kasashen nahiyar Afrika dake yankin hamada.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG