Accessibility links

Cibiyoyin Kiwon Lafiya Zasu Hada Hannu A Yaki Da HIV


Wani yana rike da allurai

Cibiyoyin kiwon lafiya da bunkasa kasa na duniya sun tsaida shawarar hada hannu a yaki da cutar kanjamau

Wata sanarwar hadin guiwa da Hukumar lafiya ta duniya (WHO),da asusun yaki da cutar kanjamau, tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro (Global Fund), da ko-odinetan shirin Majalisar Dinkin Duniya na yaki da cutar kanjamau (UNAIDS), sun bayyana bukatar hada hannu a yunkurin yaki da cutar daga yanzu.

Cibiyoyin suka ce wannan ne karon farko da cibiyoyin suka sami wata gagarumar dama ta kafa fandeshen shawo kan yada kwayar cutar kanjamau da nuna wariya da kuma shawo kan mace mace ta dalilin kamuwa da cutar. Suka kuma bayyana cewa zasu iya cimma nasara ne kawai idan cibiyoyin suka hada hannu.

Domin cimma nasara, cibiyoyin suka ce suna bukatar hada hannu sosai. Bisa ga cewarsu idan suna son su cimma nasara tilas ne su ba kasashen goyon baya domin cimma manufarsu. Suka ce wannan yana bukatar daukar matakan da zasu hada da hada hannu da al’umma da mika kai, da kuma daukar sababbin dabaru.

Tsarin “jinya 2015” tsari ne da ake maida hankali wajen ganin nasarar shirin da kuma fadada aikin. Cibiyoyin sun ce tilas ne a yi sauri domin ana kusa da kaiwa shekara ta 2015. Tsarin jinyar da hukumar lafiya ta duniya ta bayar a shekara ta 2013 kan amfani da magungunan yaki da cutar kanjamau ya hada da yin rigakafi ga wadanda suke cikin hatsarin kamuwa da cutar.

Tsarin “jinya na 2015” yana maida hankali kan hanyoyin gwaji da jinya a maimakon amfani da tsofaffin dabarun yaki da cutar.
XS
SM
MD
LG