Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Colombia da 'Yan Tawayen FARC Sun Cimma Matsayar Kawo Zaman Lafiya


Shugaban Colombia Juan Manuel Santos
Shugaban Colombia Juan Manuel Santos

Kasar Colombia ta dauki hanyar samun zaman lafiya, bayan da gwamnatin kasar da bangaren ‘yan tawayen FACR suka cimma matsayar cewa za a biya diyya ga wadanda yaki ya shafa da kuma gurfanar da wadanda suka aikata laifukan yaki a gaban kuliya.

Shugaban kasar, Juan Manuel, ya rubuta a shafinsa na Tiwtter cewa, “ba a taba samun irin wannan ci gaba ba, a kokarin da ake yi na kulla yarjejeniya.”

A baya, ‘yan tawayen FARC, sun sha alwashin ba za su amince wani daga cikinsu ya tafi gidan yari ba, sai dai a wannan yarjejeniya da aka kulla, ‘yan tawayen da suka amsa aikata laifukan yaki, sun yarda za a rinka bi-biyan duk inda suka tafi na tsawon shekaru takwas, a maimakon a rufe su a gidan kurkuku.

Sannan sun amince za su yi aikin kwashe nakiyoyin da aka dasa da kuma gudanar da ayyuka a yankunan karkara.

Baya ga haka, za a kafa wata kotu ta musamman da za ta binciki wadanda suka aikata laifukan yaki.

Yanzu haka gwamnatin ta Colombia da ‘yan tawayen, sun shata ranar 23 ga watan Maris na badi, a matsayin ranar da za a samar da cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya.

Idan dai har yarjejeniyar ta yi nasara, za ta kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 50 ana yi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 220, kana ya sa miliyoyin mutane ficewa daga gidajensu.

XS
SM
MD
LG