Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Congo Na Fama Da Ebola, Coronavirus


Yayin da take kokarin shawo kan cutar coronavirus da ta addabi duniya, kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo na fuskantar kalubalen Ebola.

Adadin mutanen da rahotanni suka ce sun kamu da cutar Ebola a yammacin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ya dara wanda aka gani a lokacin da cutar ta barke a shekarar 2018 a wannan yanki, a cewar hukumar lafiya ta duniya WHO.

A jiya Alhamis, Darektar hukumar ta WHO a nahiyar Afirka Dr. Matshidiso Moeti ta ce, “a yanzu ana da adadin mutum 56, kuma wannan babban abin damuwa ne, musamman idan aka yi la’akkari da cewa adadin ya haura 54 da aka gani a shekarar 2018.”

A cewarta, kalubalen da ake fuskanta wajen yaki da cutar ta Ebola yayin da ake kokarin dakile annobar COVID-19 ya karu, saboda rashin kudade da rashin kyawun hanyoyin isa yankin da cutar ta Ebola ke karuwa.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, idan har ba a samu karin tallafi ga fannin lafiya musamma abin da ya shafi allurar rigakafin cutar ta Ebola ba, da samar da kayayyakin gwaje-gwaje da bin diddigin wadanda suka yi cudanya da masu cutar, kudaden tallafi dala miliyan 1.75 da hukumar lafiya ta WHO ta samo, za su kare nan da wasu ‘yan makonni masu zuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG