Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus:Shugaba Trump Yana Jinya a Asibiti


Shugaban Amurka Donald Trump zai tafi jinya
Shugaban Amurka Donald Trump zai tafi jinya

An dauki shugaba Trump da jirgi mai saukar angule zuwa wani asibitin sojoji da ke kusa da fadar White House jiya Jumma’a da rana inda ake kyautata zaton zai yi jinya na ‘yan kwanaki.

Shugaban Amurka Donald Trump ya walafa sakon a shafinsa na twitter daga gadon asibiti inda yake jinya cewa, “Komi na tafiya da kyau, Ina tsammani! Na gode maku duka. KAUNA!!

https://twitter.com/realDonaldTrump/status/1312233807991496704

Kafin fita daga fadar White House ya shiga jirgi zuwa asibiti, shugaba Trump ya fitar da faifan bidiyo inda ya bayyana cewa zai tafi asibiti ya ci gaba da killace kansa.

Likitan shugaban kasar, Dr. Sean Conley, ya fada a wata wasika da ya rubutawa sakatariyar watsa labarai ta Fadar White House Kayleigh McEnany jiya Jumma’a cewa, “ A yammacin yau ina mai farin cikin sanar da cewa, Shugaban kasar yana murmurewa. Ba ya bukatar na’urar taimakawa lumfashi, sai dai bisa ga shawarar kwararru, mun fara yi mashi jinya da maganin Remdesivir. Ya kamala shan zayen farko na maganin, yana kwance yana hutawa.”

shugaban-amurka-trump-da-uwargidansa-sun-kamu-da-coronavirus

Shugaban kasar ya dagawa manema labarai hannu kafin ya shiga jirgi mai saukar angulu na shugaban kasa, Marine One zuwa fittaccen asibitin sojoji Walter Reed da ke birnin Bethesda, jihar Maryland. Asibitin yana da babban dakin zama da shugaban kasar zai iya gudanar da ayyukansa daga asibitin.

Bayan da jirgi mai saukar angulu ya isa asibitin, Shugaba Trump ya taka da kafarsa ya shiga mota da ta kai shi kofar shiga asibitin.

Bayan kwantar da Trump, Litikan shi McEnany ya fitar da sanarwa cewa, “A matsayin matakin kariya, da shawarwarin likitan shi da kuma kwararrun ma’aikatan jinya, shugaban kasar zai gudanar da aikinshi daga ofisoshin shugaban kasa da ke asibitin Walter Reed na ‘yan kwanaki.”

Shugaba Donald Trump ya isa asibitin Walter Reed bayan ya kamu da COVID-19.
Shugaba Donald Trump ya isa asibitin Walter Reed bayan ya kamu da COVID-19.

Shugaban kasar mai shekaru 74 da ke kwance a asibiti bai mika ikon shugabanci ga mataimakinsa Mike Pence ba, bisa ga cewar jami’an fadar White.

Uwargidan shugaban kasa Malania Trump wadda ita ma ta kamu da cutar ta wallafa a shafinta na twitter cewa, “kamar Amurkawa da dama, ni ma zan killace kaina sabili da kamuwa da cutar Cotonavirus. Ta kuma godewa Amurka domin jajinta masu.

Abokin hamayyar Trump dan takarar shugaban kasa na jam'iyar Democrat Joe Biden ya wallafa sakon fatar alheri ga shugaba Trump.

Shima tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya wallafa sakon gaisuwa a shafinsa na twitter inda ya bayyana cewa. “Ni da Michelle muna fatar Shugaban kasar da Uwargidansa, da dukan wadanda suka kamu da coronavirus a duk fadin kasar suna samun kulawar da suke bukata, suna kuma kan yanyar murmurewa cikin sauri.”

Shugaba Trump da Uwargidansa Malania sun fara killace kansu ne ranar Laraba kafin fitar da sakamakon gwajin cutar bayanda wata hadimar shugaban kasa Hope Hicks da ta ke tafiye tafiye tare da shi a jirgin shugaban kasa ta kamu da cutar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG