Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus Ta Hallaka Mutane Dubu Dari Biyu a Amurka


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Jiya Talata adadin wadanda cutar coronavirus ta kashe a Amurka ya kai 200,000 adadin da ya zarce na kowacce kasa a duniya, da kwararrun harkokin lafiya ke cewa adadin zai ci gaba da karuwa zuwa dubbai cikin ‘yan watanni masu zuwa.

Yawan wadanda suke mutuwa ya wuce kiyasin da aka yi tun farko kan barnar da annobar za ta yi, yawan da ya kusa ninka baki daya yawan sojojin Amurka da suka mutu a yakin da Amurka ta yi a Koriya da Vietnam da Persian Gulf da Afghanistan da kuma Iraqi, tun kawo karshen yakin duniya na biyu.

A watan Afrilu, babban masanin cututtuka masu yaduwa, Dr. Anthony Fauci, ya ce adadin wadanda zasu mutu zai iya kaiwa dubu 60, yayin da shugaban kasa Donald Trump, wanda da farko ya rage tasirin hatsarin coronavirus a matsayin irin murar da ake yi lokaci-lokaci, a watan Mayu da ce adadin wadanda za ta kashe zai kai daga dubu 75 zuwa dubu 100.

Amma yanzu, manazarta harkar lafiya a jami’ar Washington na cewa yawan mace-macen zai iya kaiwa dubu 410 ya zuwa karshen wannan shekarar da muke ciki.

Amurka dai ita ce ke da adadin mace macen coronavirus da ya zarce kowace kasa a duniya, amma a Turai da wasu kasashen Latin sun samu adadi mafi yawa idan aka kwatanta da yawan al’ummar su.

Shugaba Donald Trump bai ce uffan ba a kan adadi na tarihi a jiya Talata, maimakon haka ya maida hankali ne a kan wasu batutuwa da ya yi a shafinsa na Twitter, ciki harda batun da yake jira na cike gurbi a kotun kolin Amurka da wanda yake so, ana saura makwanni shida a yi zaben da yake neman karin wa’adi a takatar da yake yi da abokin karawar san a Democrat kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG