Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: An Sami Ci Gaba A Kasashen New Zealand Da Thailand


Kasashen New Zealand da Thailand, duk sun sanar cewa basu sami sabon kamuwa da cutar coronavirus ko daya ba a yau Laraba, a yayin da gwamnatocin kasashen suke shirin sassauta dokar hana zirga-zirga.

Wannan ne rana ta hudu irin ta da New Zealand ta samu a cikin makwanni biyun da suka gabata, wanda ya nuna alamun nasara bayan dokar kulle ta tsawon wata daya.

A ranar Alhamis za’a dauki mataki na baya-bayan nan, tare da bude kusan duk shaguna da gidajen abinci, to amma tare da kiyaye dokar ba da tazara da juna.

Ita ko kasar Thailand, wannan shine karon farko da bata samu sabon kamuwa da cutar ba tun daga watan Maris. Gwamnati ta ci gaba da jadadawa mutane mahimmancin rufe fuskarsu da abin kariya a duk lokacin da za su shiga cikin jamma’a, kana za su sake zama a ranar Jumma’a domin duba yiwuwar sassauta al’amura kamar bude manyan shaguna.

Wata alamar nasara kuma ita ce sanarwar da Australiya ta bayar a yau Laraba cewa za ta bude kan iyakarta da Jamus daga ranar 15 ga watan Yuni bayan da shugabannin kasashen suka gana.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG