Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19 Wani Mummunan Abu Ne - Anthony Fauci


Anthony Fauci
Anthony Fauci

Dr. Anthony Fauci ya bayyana annobar cutar COVID-19 a matsayin wani "mummunan abu" a lokacin da ya ke jawabi jiya Talata ga wasu shugabannin masana’antun nazarin ilimin hallita na zamani, a cewar wani rahoto.

“A cikin wata hudu, annobar ta gurgunta lamura a fadin duniya, kuma har yanzu ba ta wuce ba,” abinda Fauci, daraktan cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta Amurka ya fadi kenan a wani rahoto da aka wallafa a jaridar New York Times.

COVID-19 cuta ce da coronavirus ke janyowa, cutar da ke shafar numfashin bil’adama, da ake dauka daga mutum zuwa mutum, wadda kuma ya zuwa yanzu mutum sama da miliyan 7 suka kamu da ita a duniya, ta kuma kashe sama da mutum 408,000.

Fauci ya ce, yanayin da cutar ke yaduwa cikin sauri a duniya ya bada mamaki, ya kara da cewa, cuta mai yaduwa za ta iya bazuwa a fadin duniya cikin wata shida zuwa shekara daya.

"Amma wata guda COVID-19 ta ɗauka," inij Fauci a cewar rahoton.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG