Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: ‘Yan Kasuwa a Kano Na Neman Tallafin Gwamnatin Tarayya


'yan kasuwa sun yi gangami a kano

‘Yan kasuwa a jihar Kano sun bukaci tallafin gwamnatin tarayya domin farfado da hannayen jarinsu na kasuwanci saboda mawuyacin hali da suka shiga sanadiyyar cutar corona, yayin da masana tattalin arziki ke shawartar hukumomin najeriya su habaka harkokin kasuwar cikin gida.

Kimanin makonni biyu bayan shugaba Buhari ya soke dokar kulle a wasu manyan biranen kasar, gwamnonin Kano da Kaduna na ci gaba da aiki ta wannan dokar, a wani mataki na ci gaba da yaki da cutar corona.

Koda yake gwamnonin sun sassauta dokar domin baiwa jama’a musamman ‘yan kasuwa damar hada hada a wasu ranaku da aka kebe, amma ‘yan kasuwa a Kano na neman Kari, kamar yadda shugaban ‘yan kasuwar Kantin kwari Alhaji Shariff Sagir ya fadawa Muryar Amurka.

Baya ga karancin ranakun hada hada, karayar jari saboda illar corona shine babban al’amarin da ke ciwa ‘yan kasuwar tuwo a kwarya don haka suka nemi agajin shugaba Buhari.

Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da masana tattalin arziki ke jan hankalin hukumomin Najeriya su habbaka lamuran kasuwanin su na cikin gida a matsayin matakin tada komar tattalin arziki.

Ga Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00


Facebook Forum

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG