Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cyril Ramaphosa Ya Zama Shugaban Afrika Ta Kudu


Sabon Shugaban Afrika Ta Kudu
Sabon Shugaban Afrika Ta Kudu

Kasa da sa’oi 24 bayan murabus din Jacob Zuma, Afrika ta Kudu tayi sabon shugaban kasa. Cyril Ramaphosa, wani fitaccen dan kasuwa da kuma kusa a jam’iyar African National Congress ANC, wanda ya taka rawar gani a tilastawa Zuma ajiye aiki.

An rantsar da Ramaphosa ranar alhamis a birnin Cape Town bayanda majalisa ta zabe shi babu hamayya.

An rantsar da shi ne bayan misalin sa’oi 12 da yin murabus din Zuma, biyo bayan matsin lamba da ya fuskanta daga jam’iyarsa da ya sauka daga karagar mulki kafin cikar wa’adin mulkinsa a tsakiyar shekara ta dubu biyu da goma sha tara.

Ramaphosa ya bayyana cewa, zai fuskanci kalubalai masu yawa a sabon mukamin da suka hada da yaki da cin hanci da rashawa da yayi kamari a jam’iyarshi, da kokarin cike gibin dake akwai na tattalin arziki tsakanin ‘yan kasa bayan karshen mulkin wariyar launin fata, da kuma ci gaba da sabon aikinsa lokacin da za a gudanar da zaben kasa a shekara ta dubu biyu da goma sha tara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG