Yanzu akwai wahala ace an ceto demokaradiyya a cikin kasar Cambodia, a cewar wata shugabar jamiyyar National Resource Party (CNRP) Mo Sochua, wadda ta ce a ranar tarlata data gabata ta dauki wannan mataki domin ta samu labarin cewa ba makawa ita ma za a kama ta.
Idan ba demokaradiyya, sai kokarin bita da kulli da kame mutane a tsare, to akwai bukatar samun wani zabin abin yi akan wannan lamari ta yadda za a ciyar da demokaradiyya gaba tare da ceto ta daga rugujewa a cikin kasar mu inji Mo Sochua wadda take Magana daga wata kasar wajen da ba a san ko ina take ba.
Facebook Forum