Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu A Turkiyya Ta Yankewa Mutane 34 Hukuncin Daurin Rai Da Rai


Yau Laraba wata kotun kasar Turkiyya ta yankewa mutane 34 hukuncin daurin rai da rai a gidan yari

Kotun ta yanke wa mutanen hukuncin ne a sakamakon samun su da laifin kitsa makarkashiyar yiwa shugaba Recep Tayyip Erdogan, kisan gilla a lokacin wani yinkurin juyin mulki wanda bai yi nasara ba a shekarar da ta gabata.

Cikin wadanda aka yankewa hukuncin harda manyan jami’an soja masu mukamin Janar da anini, da aka ce suna da hannu a wani samame da aka kai a Otel din da Erdogan da iyalinsa suke ciki a daren da aka yi yinkurin juyin mulkin wanda bai yi nasara ba. Erdogan da iyalansa sun tsallake rijiya da baya bayan da sojojin suka kutsa Otel din.

Mutane dayawa da ake tuhuma bisa yinkurin juyin mulkin sun ce ba a yi masu adalci ba kuma an gallaza masu a lokacin da suke tsare.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG