Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Dan Gari: Tarihin Masarautar Lere, Kaduna


A wannan makon gidan rediyon Vision FM ya kai ziyara masarautar Lere da ke gabashin jihar Kaduna a Najeriya don jin tarihinta.

Masarautar Lere a jihar Kaduna na kunshe da gundumomi 9 da kauyuka da dama, galibin mazauna masarautar manoma ne, da makiyaya da kuma masunta. Lere dai kalma ce fulatanci da ke nufin mazaunin din din din.

Malam Muhammadu Dabo Titi, bafullatanen Winti daga kasar Bauchi, shi ne ya kafa garin a shekarar 1808.

Isma'ila Umar, Dan Isan Lere, ya bada takaitaccen tarihin garin da kuma kalubalen da al'umar garin ke fuskanta. Ya bayyana cewa Tambura na daga cikin abubuwan tarihin da masarautar Lere ke tunkaho da shi.

Saurari shirin cikin sauti wanda Muslim Muhammad Yusuf ya gabatar.

Da Dan Gari: Tarihin Masarautar Lere, Kaduna
please wait

No media source currently available

0:00 0:08:25 0:00


XS
SM
MD
LG