Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya ba jami’an tsaron kasar izini yau asabar su ci gaba da kai farmaki kan kungiyoyin mayaka, abinda ya kawo karshen tsagaita wuta na kwanaki goma sha takwas da aka yi da Tabilan.
Gwamnatin ta tsaida shawara ta kashin kanta, ta tsagaita yaki da kungiyar Taliban a kasar na tsawon mako guda kwanaki biyu kafin ranar goma sha biyar ga watan Yuni da aka yi bukin sallah.
Daga baya Ghani ya kuma kara wa’adin tsagaita wutar da kwanaki goma da begen zai karfafawa kungiyar Taliban guiwa,ta daina tashin hankali, ta kuma nemi zaman tattaunawa da zata kawo karshen yakin Afghanistan.
Kungiyar Taliban karon farko cikin shekaru goma sha bakwai, ta tsagaita kai hare hare lokacin bukukuwan sallah na tsawon kwanaki uku. Sai dai kungiyar tayi watsi da kiran da shugaban Ghani ya yi na kara wa’adin tsagaita wutar, kuma tuni ta ci gaba da kai hare hare kan jami’an tsaron Afghanistan dake janyo asarar rayuka.
Rundunar sojin Amurka ma ta goyi bayan dakarun Afghanistan tare da tsagaita kai hare hare ta jiragen sama kan kungiyar Taliban, a lokacin da dakarun gwamnati suka tsagaita wutar. Ghani ya sake mika goron gayyata ga kungiyar mayakan da neman tazo teburin tattaunawar zaman lafiya.
Facebook Forum