Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Ta Kashe Sojojin Afghanistan 30


Sojojin Afghanistan
Sojojin Afghanistan

Wani hari da Taliban ta kai da sanyi safiyar yau Laraba a gabashin Afghanistan, ya kashe mutane 30 a cikin rundunar gwamnati, mummunar hari tun bayan da aka tsagaita bude wuta na wucin gadi domin gudanar da bukuwar karamar Sallah.

Jami'an cikin gida sun ce mayakan sa kan Taliban sun kai harin ne a tungar rundunar gwamnati ta ANA a yankin Bala Murghab dake cikin gundumar Badghis, lamarin da ya haddasa arangama a wurin kuma an kashe mayaka na kowane bangarorin.

Gwamnan gundumar Abdul Ghafoor Malikzai, ya fadawa Muyar Amurka, an kashe sojoji 30 na rundunar ANA da suke kan hanyarsu zuwa inda ake yakin, yayin da mayakan Taliban suka musu kwantan bauna

Mai Magana da yawun ma'aikatar tsaro a Kabul ya fadawa Muryar Amurka cewa fadar tayi sanadiyar mutuwar sojojin Afghanistan 13 kana wasu takwas suka ji rauni.

Taliban ta kawo karshen shirinta na tsagaita wuta na kwanaki uku ne a ranar Lahadi, yayin da gwamanti ta kara lokaci zuwa mako daya, amaimakon ya kare yau Laraba, wato zuwa kwanaki goma. Wannan ne karo na farko a cikin shekaru 17 da bangarori masu yaki da juna a Afghanistan suka tsagaita wuta na dan lokaci.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG