Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Najeriya Sun Fatattaki Boko Haram


Hukumar NEMA tace dama tana cikin shirin ko ta kwana saboda mutane masu rauni kamar mata, yara da tsofaffi

Kamar yadda rahotannin dake fitowa daga yankin na Madagali dake arewacin jihar Adamawan ke nunawa, kawo yanzu hankula sun fara kwantawa biyo bayan nasarar da dakarun Najeriya tare da tallafin yan sakai na maharba suka samu wajen fatattakar yan bindiga masu tada kayar bayan na Boko Haram.

Ko da yake kawo yanzu ba’a kammala tantance alkalumman wadanda aka kashe ba,kama daga bangaren fararen hula ,sojoji dama na yan sakan, shugaban karamar hukumar Madagalin Yusuf Muhammad yace mace guda ce ta rasa ranta cikin tsautsayi.

Yayin dama hankulan ke kwantawa , hukumar bada agajin gaggawa a Najeriya,NEMA tuni ta tura jami’anta don duba halin da ake ciki.Bashir Idris Garga dake zama jami’in hukumar ta NEMA, mai kula da shiyar Yola,da ta kunshi jihohin Adamawa da Taraba ya bayyana matakan da suka dauka.

Cikin kwanakin nan dai yankin na Madagali na fama da hare haren mayakan na Boko Haram lamarin da ke kara tada hankulan al’ummomin da suka koma yankunansu da aka kwato.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG