Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Somaliya Sun Kashe Wasu Mayakan Kungiyar al-Shabab


Wasu mayakan al-Shabab
Wasu mayakan al-Shabab

A Somalia, sojojin kasar sun kashe mayakan sakai na al-Shabab, suka kuma gano makamai da albarusai, a wani matakin soja da suka dauka jiya Laraba a tsakiyar kasar, kamar yadda jami'an gwamnati da mazauna yankin suka bayyana.

Wani sojan kasar mai mukamin kanar, Ahmed Mohammed, ya gayawa Sashen harshen Somalia na Muryar Amurka cewa, sun kai somamen ne a wani wuri kusa da garin Masagawa wanda yake kusa da El-Dheer, a yankin da ake kira Galgadudd. Yace an kashe sojan gwamnati daya a matakin.

Mazauna Masagawa sun gayawa Sashen Somaliyacewa, sun ji karar wasu fashe fashe masu karfin gaske, yayinda sojojin gwamnati suke gwabzawa da mayakan sakan na al-Shabab.

An dauki wannan matakin ne a dai dai lokacinda shugabannin gwamnatin kasar da na jihohi suke wani taro a Baidoa, babban birnin lardin yankin Bay,dake kudu maso yammacin kasar, domin su tattauna kan batun tsaro lokacin zaben kasar da aka ayyana cikin watan Agustan bana.

XS
SM
MD
LG