Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilan Koma Bayan Man City


Filin Wasan Manchester City
Filin Wasan Manchester City

Manazarta lamurran wasanni na bayyana ra’ayoyin su akan koma bayan da kungiyar Manchester City ta Ingila ke fuskanta, a daidai lokacin da ake soma sabuwar kakar wasanni ta shekara ta 2020/2021.

A jiya Lahadi kungiyar ta sha kashi a cikin gidanta, inda Leicester City ta lallasa ta da ci 5-2, a wasansu na biyu na gasar Premier ta wannan shekara.

Kakar wasannin da shige ne kadai marabinsu da kofin gasar ta Premier, wadda suka lashe a shekarar 2018, suka kuma lashewa a shekarar 2019, to amma masu sharhi akan lamurran wasanni na ganin kungiyar na fuskantar koma baya a wannan kakar wasannin.

'Yan Wasan Manchester City
'Yan Wasan Manchester City

To sai dai kuma wasu na ta’allaka matsalolin da kungiyar ke fuskantar a ‘yan kwanan nan da rashin wasu jiga-jigan ‘yan wasan ta kamar Sergio Aguero da Gabriel Jesus, wadanda yanzu haka suke jiyyar raunuka na tsawon makwanni.

To sai dai duk da haka wasu na dora alhakin ne kan dabarun mai horar da ‘yan wasan kungiyar Pep Guardiola, da kuma yadda yake amfani da ‘yan wasan, wanda ake ganin ba ya kai kungiyar ga samun nasara.

Facebook Forum

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG