Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa APC Ta Fadi Zabe a Osun - Masharhanta


Malaman zabe suna kidaya kuri'u a zaben Najeriya
Malaman zabe suna kidaya kuri'u a zaben Najeriya

Bayan da Jam’iyar PDP mai adawa ta lashe zaben sanata a mazabar Osun ta yamma dake jihar Osun a kudu maso yammcin Najeriya, masu fashin baki a fannin siyasa na ganin sakamakon zaben tamkar zakaran gwajin-dafi ne ga zabuka dake tafe ga jam’iya mai mulki ta APC, lamarin da su ke ganin ya jefa fargaba a zukatan mabiyanta.

Masu lura da al’amura da dama sun yi hasashen cewa jam’iyar mai mulki ta APC ce za ta lashe zaben mazabar Osun ta yamma, lura da cewa ita ce ke mulkar jihar, amma sai reshe ya juye da mujiya.

Dan takarar jam’iyar ta PDP Ademola Adeleke, kani ga Isiaku Adeleke da ya rasu ya bar gurbi, shi ya lashe zaben.

Ademola ya samu kuri’u 97,480 yayin da abokin hamayyarsa na APC Mudashiru Hussein ya samu kuri’u 66,116.

“Bayan da Ademola Adeleke na jam’iyar PDP ya cika sharuddan da shari’a ta gindaya na samun kuri’u mafiya rinjaye, ya zama shi ne ya yi nasarar lashe zabe.” In ji babban jami’in hukumar zabe ta INEC a jihar ta Osun, Farfesa Layede Lawal.

Shi dai Mudashiru shi ne zabin gwamnan jihar Rauf Aregbesola, kuma da yawa na yi wa sakamakon zaben kallon zakarin gwajin-dafi ga gwamnatin jihar.

Ademola wanda a da dan jam'iyar APC ne, ya nemi tikitin neman tsayawa takarar a karkashin jam'iyar, amma sai aka hana shi tikiti, lamarin da ya sa ya sauya sheka ya koma PDP inda suka tsayar da shi a matsayin dan-takararsu.

Masharhanta a jaridun Najeriya da dama, kamar jaridar Punch da ake bugawa a kudancin Najeriya, sun ce al'umar jihar da dama sun yi tsammanin jam'iyar ta APC za ta tausaya ta bai wa Ademola tikitin takarar saboda rasuwar wansa, sai ta bai wa Mudashiru - zabin Aregbesola.

A watan Afrilun shekarar nan Sanata Isiaku Adeleke na jam’iyar PDP dake rike da kujerar a majalisar dattawa ya rasu, lamarin da ya haifar da gurbi.

Yanzu kaninsa Ademola Adeleke, wanda ya lashe zaben, zai rike mukamin har zuwa 2019 da za a sake sabon zabe.

Saurari rahoton wakilin Muryar Amurka daga Ibadan, Hassan Umaru Tambuwal domin jin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG