Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Jacob Zuma Ya Mika Kansa


JACOB ZUMA
JACOB ZUMA

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya mika kansa ga ‘yan sanda a safiyar yau Alhamis don fara zaman gidan yari na tsawon watanni 15.

'Yan mintoci kaɗan kafin ‘yan sanda su kama shi da tsakar dare, Zuma ya bar gidansa na Nkandla a cikin jerin gwanon motoci.

Zuma ya yanke shawarar mika kansa ga hukumomi ne don yin biyayya ga umarnin daga babbar kotun kasar, Kotun Tsarin Mulki, cewa ya kamata ya yi zaman gidan yari saboda raina kotu da ya yi.

"Shugaba Zuma na kan hanyarsa ta mika kansa ga wani sashin kula da ayyukan gyara a KZN (lardin KwaZulu-Natal)," in ji wani sako da Gidauniyar Zuma ta wallafa a Twitta.

Jim kadan bayan hakan, ‘yan sandan Afirka ta Kudu sun tabbatar da cewa Zuma din na hannunsu.

Zuma ya yanke shawarar yin biyayya ga umarnin Kotun Tsarin Mulki ne bayan mako guda na tashe-tashen hankula game da hukuncin daurin da aka yi masa.

An yanke wa Zuma hukuncin daurin watanni 15 a kurkuku ne saboda rashing jin umarnin kotu da ya ba shi na ya shaida a gaban kwamitin shari'a da ke binciken zarge-zargen cin hanci da rashawa a lokacin da yake shugaban kasar, daga 2009-18.

Kotun tsarin mulki ta ba da umarnin cewa idan Zuma bai mika kansa ga ‘yan sanda ba, ‘yan sanda su kamo tsohon shugaban kasar kafin karshen ranar Laraba.

XS
SM
MD
LG