Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa PDP Take So A Hana Tinubu, Obi Takara A Zaben 2023


Wani taron PDP da ta yi a baya (Instagram/PDP) an yi amfani da wannan hoto don nuna misali.
Wani taron PDP da ta yi a baya (Instagram/PDP) an yi amfani da wannan hoto don nuna misali.

PDP ta shigar da karar ce a wata babbar kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Babbar jam’iyyar adawa ta Peoples’ Democratic Party a Najeriya (PDP), ta shigar da jam’iyyar APC mai mulki da Labour Party kara a wata kotu da ke Abuja.

PDP ta nemi kotun ta tilasta hukumar zabe ta INEC ta haramtawa jam’iyyun biyu sauya ‘yan takarar mukamin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima (APC) da Datti Baba-Ahmed na (LP)

Karar da PDP ta shigar har ila yau tana neman kotun ta haramtawa Bola Ahmed Tinubu da Peter Obi yin takara a zaben na 2023, saboda sun sauya abokanan takararsu.

A makon da ya gabata, Tinubu ya bayyana sunan tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda zai maye gurbin Alhaji Kabiru Masari.

Gabanin hakan APC ta ba da sunan Masari a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na rikon kwarya.

Sai dai Masari ya janye daga takarar tasa a makon da ya gabata, jim kadan kuma Tinubu ya bayyana sunan Shettima a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Kazalika jam’iyyar LP ita ma ta sauya Doyin Okupe da Baba-Ahmed a makon da ya gabata, inda da farko sunan Okupe jam’iyyar ta mika a matsayin dan takarar rikon kwarya a mukamin mataimakin shugaban kasa.

Sai dai a bukatun da ta nema, jam’iyyar ta PDP ta yi kira ga kotun da ta tilasta hukumar zabe ta INEC ta haramtawa Tinubu da Obi takarar shugaban kasa, har sai sun amince za su yi takara da zabinsu na farko, wato Tinubu da Masari a APC sai kuma Obi da Okupe a LP.

PDP ta gabatar da hujjar cewa, a dokar Najeriya, babu inda aka ba da hurumin a tsayar da dan takarar mataimakin shugaban kasa a mataki na wucin gadi.

XS
SM
MD
LG