Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa ‘Yan bindiga Suka Fitini Garin Zaria – Gwamnatin Kaduna


Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli.
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli.

A ranar Juma’a ‘yan bindiga suka kashe dalibi daya suka jikkata wani sannan suka sace mutum takwas ciki har da malamai biyu a kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamallin da ke Zaria a jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya.

A ‘yan kwanakin nan ‘yan fashin daji da ke kai hare-hare a wasu sassan jihar Kaduna, sun karkata hankulansa yankin Zaria inda a baya-bayan nan suka sace dalibai da malamansu a kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke birnin na Zaria.

Hakan ya sa, masarautar ta Zaria ta nuna damuwarta kan yadda al’umar yankin ke bacci da ido daya kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito Mai Martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli yana fada yayin wata ziyarar da manyan jami’an tsaron jihar da na gwammati suka kai fadarsa.

Kofar Kwalejin Kimiyya ta Nuhu Bamalli a Kaduna (Hoto: Facebook/ Channels TV)
Kofar Kwalejin Kimiyya ta Nuhu Bamalli a Kaduna (Hoto: Facebook/ Channels TV)

A cewar Sarki Bamalli, duk da cewa akwai manyan cibiyoyin tsaro da makarantun horar da sojoji a yankin, masarauatar ba ta tsira daga hare-haren masu garkuwa da mutane ba, lamarin da ya ce ya ta’azzara a ‘yan kwankin nan kamar yadda jaridar ta Trust ta ruwaito.

Karin bayani akan: Sarkin Zazzau, Nasiru El Rufai, Samuel Aruwan, Kaduna, Zaria, Daily Trust, Channels TV, Nigeria, da Najeriya.

A ranar Juma’a ‘yan bindiga suka kashe dalibi daya suka jikkata wani sannan suka sace mutum takwas ciki har da malamai biyu a kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamallin da ke Zaria.

“An tura dakarun Najeriya akan hanyar Kaduna zuwa Zaria, suna kuma yaki da ‘yan bindigar tare da yin sintiri a yankin,” Kwamishan tsaron cikin gida Samuel Aruwan ya fadawa Channels TV jim kadan bayan sace daliban da aka yi.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan
Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan

A cewar Samuel Aruwan, dalilin da ya sa ‘yan bindigar suke yawan kai hare-hare a yankin garin na Zaria shi ne, an dakile walwalar da suke samu akan babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria.

“Mun yi imanin cewa, ‘yan bindigar sun je kwalejin ne, saboda an hana su sakat akan wannan hanya, shi ya sa suka far wa makarantar.”

A cewar Aruwan, gwammatin na daukan dukkan matakan da suka dace wajen ganin an samar da cikakken tsaro a yankin.

Sarki Bamalli ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su yi bakin kokarinsu wajen ganin sun samar da tsaro a yankin.

A baya, ‘yan bindigar kan mayar da hankalinsu kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ne, amma a baya-bayan nan, ayyukansu sun fi karkata akan hanyar Kaduna zuwa Zaria.

Sojojin Najeriya yayin wani atisaye da suka yi (Twitter/@HQNigerianArmy)
Sojojin Najeriya yayin wani atisaye da suka yi (Twitter/@HQNigerianArmy)

Baya ga daliban na Nuhu Bamalli, a watan Maris ‘yan fashin daji suka sace dalibai a kwalejin horar da ilimin gandun daji da ke Afaka, wadanda aka sako a ‘yan makonnin baya.

A watan Afrilu kuma an sace wasu dalibai a Jami’ar Greenfield da ke Kaduna, wadanda aka sako su a baya-bayan nan, yayin da wasu suka rasa rayukansu a hannun ‘yan bindigar.

Gwamna Malam Nasiru El Rufai na Kaduna, ya ce gwamnatinsa ba ta yadda da biyan fansa ko yin sulhu da ‘yan bindiga ba, lamarin da ke ci gaba da janyo ka-ce-na-ce a tsakakin mazauna yankin.

XS
SM
MD
LG